23.4 C
Kano
Thursday, December 18, 2025

Bai kamata Tinubu ya tsaya takarar Shugaban Kasa a 2027 ba: Datti Baba Ahmed

Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party (LP), ya shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya nemi sake tsayawa takara a 2027 idan har yana da basirar siyasa kamar yadda ake cewa.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa na tashar Arise TV mai suna Prime Time a ranar Juma’a, inda ya ce lokaci ya ƙure wa Tinubu, kuma komai yana bayyane ga shi da kuma jam’iyyarsa ta APC cewa za su sha kaye a zaɓen 2027.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na LP a 2023 ya bayyana cewa APC za ta sha kaye a zaɓen 2027. Ya ce ‘yan Najeriya za su haɗu guri guda domin su kada ƙuri’ar kawar da shugabanni marasa nagarta.

 

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa