Shugabar hukumar yaƙi da cutar AIDS ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu kusan mutum miliyan tara da za su kamu da cutar ta HIV nan da shekara huɗu masu zuwa saboda dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa a bangaren kiwon lafiya
Da take jawabi a Geneva, Winnie Byinyama, ta ce za a samu sabbin masu kamuwa da cutar aƙalla guda 2,000 kullum saboda janye tallafin – ta ce tuni dubban likitoci da sauran ma’aikatan jinya sun fara rasa aikinsu.
Sai dai duk da haka ta yaba da gudumawar Amurka wajen tallafa wa ayyukan kiwon lafiya a duniya a gomman shekaru da suka gabata.
Amma ta ce yadda kwatsam aka dakatar da tallafin ba tare da shiri ba, ya fara kawo tsaiko a ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da cutar ta HIV.