24.4 C
Kano
Thursday, December 19, 2024

DSS sun kashe daya daga cikin ‘yan bindigar da suka sace mahaifiyar Rarara

Jami’an rundunar tsaron farin kaya ta DSS sun kashe daya daga cikin ‘yan bindigar da suka sace mahaifiyar mawakin nan Rarara tare da kama 1 daga cikin maharan a wani musayar wuta da suka yi.

Jaridar Kakaki 24 ta ruwaito Wata majiya daga rundunar DSS ta ce jami’an tsaron su dira a maboyar ‘yan bindigar dake dajin Makarfi a jihar Kaduna da safiyar ranar Juma’a a yayin da ‘yan bindigar ke raba kudin fansa da suka karba.

Acewar majiyar: “Jami’an sun yi galabar fin karfin ‘yan bindigar inda suka kashe daya nan take da kuma kama 1 wanda ke karbar magani saboda harbin bindiga sannan an kwato Naira Miliyan 26.5 daga wurinsu”.

Ya ce an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri da bibiyar ‘yan bindigar zuwa dajin Makarfi.

Ya ce: ” Samamen yayi nasara inda daya dan bindigar ke taimakawa da bayanan sirri kan yadda suke garkuwa da ‘yan Najeriya

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa