21.5 C
Kano
Wednesday, December 17, 2025

ENGINEER ABBAN BICHI Zai Bunkasa Ayyukan Ungozomomi da Dakile Haihuwar Bakwaini a Karamar Hukumar Bichi…

A yunkurinsa na ingantawa da kuma bunkasa kiwon lafiya ga al’ummar Karamar Hukumar Bichi, Maigirma Dan’Majalisar Tarayya na Bichi kuma Shugaban Kwamitin kasafin kudi na majalisar tarayya dake Abuja, Engineer Abubakar Kabir Abubakar Bichi wato Abban Bichi ya shirya tsaf domin gudanar da bunkasa ayyukan ungozomomi da kuma dakile haihuwar bakwaini a fadin Karamar Hukumar Bichi ta Jihar Kano.

Bayanan haka sunfito daga Shugaban Kwamitin Kiwon Lafiya na shi Maigirma Dan’Majalisar wato Farfesa Yusuf Mohammed Sabo a wata takarda daya rabawa manema labarai a yau Lahadi a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Farfesa Sabo yace wannan Kwamiti na lafiya abisa sahalewar Maigirma Member sun shirya domin zakulo mata masu karbar haihuwa wato ungozomomi a mazabu goma shada na Karamar Hukumar Bichi domin horar dasu hanyoyin karbar haihuwa na zamani cikin tsabta. Sannan
kuma kwamitin zai daga darajar mata da dama wanda suka dade suna karbar haihuwa a gargajiyance domin horar dasu da kuma basu kayan aiki.

Haka kuma Maigirma Member, Abban Bichi, ya bada umarni ga kwamitin daya fito da hanyoyi na dakile haihuwar bakwaini wanda tuni kwamitin yayi nisa domin gudanar da fara wannan aikin a dukkan mazabun mu goma shada da kuma samar da kwaleban renon jarirai (Incubators) a babban asibitin masarauta na cikin garin Bichi.

Farfesa Sabo daga karshe ya yabawa Honorable Abba Bichi a matsayin Dan’Majalisa daya tilo da a kullun yake kokarin inganta kiwon lafiya a mazabarsa ta Bichi dake Jihar Kano.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa