Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya roki mambobin jam’iyyar da su nisanci duk wani abu da zai janyo rabuwar kai ko tayar da kura a cikin jam’iyyar, musamman kan batun tabbatar da nadin Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban Hukumar Kula da Harkokin Lantarki ta Kasa (NERC).
A wata sanarwa da aka aikowa Kadaura24, Abdullahi Abbas ya nuna damuwa kan yadda cece-kuce kan lamarin ke kara raba kan mambobin jam’iyyar da kungiyoyin magoya bayan su a jihar.
Ya ce maganganun da ke fitowa daga bangaren magoya bayan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da kuma na mabiyan tsofaffin ’yan takarar gwamna da mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Hon. Murtala Sule Garo ba su da amfani ga zaman lafiya da hadin kan jam’iyyar.
Ya jaddada cewa nadin shugaban NERC batu ne da ya rataya a kan ikon Shugaban Kasa tare da amincewar Majalisar Dattawa, don haka ya kamata a bar su su gudanar da aikin nasu bisa doka da tsarin mulki.
Shugaban jam’iyyar ya tunatar da mambobi cewa, duk da bambancin ra’ayi da siyasar jam’iyya ke tattare da shi, APC ta dade tana tafiya bisa akidar hadin kai da zaman lafiya. Don haka ya bukaci kowa da kowa ya zauna lafiya, ya mutunta doka, sannan ya guji kalaman da ka iya haddasa rikici.
A cewarsa, yana da yakinin cewa Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Kasa za su dauki matakin da ya dace wanda zai fi amfani ga al’umma da jam’iyyar baki daya


