Kungiyar dake bibiyar kasafin kudin harkokin lafiya musamman akan mata da kananan yara Africa Health Budget Network ta bukaci gwamnati da rika sakin kudaden gudanar da alluran rigakafi akan lokaci.
Mai kula da kungiyar shiyar Kano Dr Musa Bello ne ya bayyana hakan yayin taron manema Labarai da suka gudanar anan Kano
Dr Musa Bello ya ce duk da gwamnati na sakin kudade don tafiyar da harkokin lafiya musamman na alluran rigakafi akwai bukatar rika sakin kudaden Akan lokaci
Yace sun shirya taron manema labaran ne don bayyana kokari da kungiyar takeyi da hadin gwiwar Afenet don tabbatar da cewa ana shawo kan matsaloli da suka donganci allurar rigakafin kananan yara
Dr Musa Bello ya kuma bayyana cewa kungiyoyi dake tallafawa jihar Kano kan harkokin alluran rigakafi yana da kyau su rika hada kawunan su don samun cigaba
Kungiyar ta Africa Health Budget network a yanzu haka tana aiki a kasashe guda shida da ke afirka Wanda aka fara a shekarar 2023
taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki Akan harkokin alluran rigakafi da dama daga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu