17.9 C
Kano
Thursday, December 18, 2025

Majalisar Dattawa ta amincewa Tinubu naɗin mutane 5 a matsayin kwamishinonin INEC ciki harda dan Kano

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tabbatar da mutanan ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin kan hukumar zabe na majalisar dattawa.

Shugaban kwamitin Sanata Simon Lalong na jam’iyar APC daga jihar Plateau ne ya gabatar da rahoton.

Sabbin kwamishinonin hukumar zaben sun hada da Alhaji Umar Yusuf Garba, daga jihar Kano,da Sa’ad Idris daga Bauchi da Chukwemeka Ibeziako daga Anambra da Umar Mukhtar daga jihar Borno da Dr Johnson Sinkiem daga Bayelsa.

Lalong, a cikin jawabinsa, ya ce kwamitin ya yi la’akari da kwarewar aiki da kuma nagartar mutanan kafin amincewa dasu.

Majalisar ta dogara ne da ne da sashe na 154(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 wajen amincewa da mutanan.

A ranar 18 ga watan maris na shekarar 2025 Tinubu ya aike da sunayen mutanan zuwa majalisar dattawa

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa