16.9 C
Kano
Tuesday, January 20, 2026

Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi ga gwamnatin Jigawa

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara, ya mayarwa baitul malin jihar Naira miliyan 301 da su ka yi ragowa bayan kammala shirin ciyarwa na watan Ramadan bana.

Sankara ya sanar da mayar da kudaden ne a yayin taron majalisar zartarwa na jiha wanda gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranta.

Kudin sun yi ragowa ne biyo bayan ware naira biliyan 4.8 da gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa ma’aikatar don shirin ciyar da abinci, wanda ya kunshi dukkanin kananan hukumomi 27 da kuma cibiyoyi kusan 700 na ciyarwa.

An ba da rahoton cewa, shirin wanda wani kwamiti ya jagoranta, ya ciyar da mutane sama da 5,550 a kullum a tsawon kwanaki 29 na azumi.

Majalisar zartaswar jihar ta yaba wa matakin da kwamishinan Sankara ya dauka na dawo da ragowar kuɗin, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abin yabawa da nuna gaskiya da rikon amana da kuma tattalin dukiyar al’umma

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa