14.9 C
Kano
Tuesday, January 20, 2026

Bama Bukatar Kwankwaso ya shigo APC

Ƙungiyar Ɗaliban Jam’iyyar APC na Kano (KASASCO) ƙarƙashin jagorancin Comrade Yahaya Usman Kabo sun bayyana rashin goyon bayan tsohon gwamnan Kano Engr Rabi’u Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyar APC.

Yayin taron manema labarai da ƙungiyar suka yi, sun ce ganin yadda a yanzu jam’iyyar NNPP ta zaizaye sakamakon Sanatan Kano ta Kudu, Sen. Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila da Rt Hon. Kabiru Alhassan Rurum, da Hon. Abdullahi Sani Rogo, da Sha’aban Sharaɗa da Hon. Zubairu Hamza Massu da Hon. Muhammad Diggol da Tsohon Sakataren Gwamnati Abdullahi Baffa Bichi da Abbas Sani Abbas, waɗanda suka taka rawa wajen NNPP ta samu nasara a yanzu sun dawo jam’iyyar APC ba su ga dalilin da Kwankwaso zai dawo jam’iyyar APC a yanzu ba

Kabo, ya ƙara da cewa ganin yadda Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ke ci gaba da zabarin sauran ƴan jam’iyyu a Kano, kuma a yanzu babu jam’iyyar da ke samun karɓuwa sama da APC bai ga dalilin Kwankwaso ya ce zai shigo jam’iyyar ba.

Daga karshe ƙungiyar ta KASASCO ta yabawa jagororin APC na Kano yadda suke kokarin ɗinke duk wata ɓaraka da kuma wakilcin da suke yi wanda suke sauke nauyin da al’umma suka dora musu.

Labarai masu alak'a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Kasance tare da mu

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe

Sababbin Wallafa