Kamfanin albarkatun man fetur na Nigeria NNPCL ya rage farashin man fetur daga Naira 960 zuwa N945.
Kadaura24 ta tabbatar da hakan ne bayan da ta gudanar da bincike a wasu gidajen man NNPC dake birnin Kano.
Idan za’a iya tunawa matatar mai ta Dangote a makon nan da muke bankwana da shi ta sanar da rage farashin man zuwa N835 mai makon yadda take sayarwa a baya.
Sai dai bincike ya gano cewa Kamfanin NNPC din bai sanarwa al’umma raginba, amma ya rage farashin man akan kawunan da yake sayar da man a gidajen mai mallakin kamfanin.


