APC ta magantu akan jita-jitar cewa shugaban ƙasa Tinubu zai canja Kashim Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027.
APC, ta kuma musanta rade radin cewa akwai sabani tsakanin Shugaban ƙasa Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.
APC tace babu wani shirin da shugaban Najeriya Tinubu keyi na canja Kashim Ibrahim gabanin zaɓen shekarar 2027.
Daraktan yaɗa labarai na jam’iyar Alhaji Bala Ibrahim, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis lokacin da yake zantawa da jaridar Daily trust.
Daraktan yaɗa labaran yace maganganun da ake yadawa basu da tushe balle Makama.
Bala Ibrahim ya ƙara da cewa ko da Tinubu yana da niyyar sauya mataimakin nasa ba zai yi hakan shi kadai ba, yana mai cewa wajibi ne a tattauna da manyan jiga-jigan jam’iyya kafin daukar irin wannan mataki.