Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi.
Wazirin Sakkwato, ya yi addu’a Allah Ya taimaka musu a wannan muhimmin aikin na addini da suke yi.
Idan aka dace da ganin watan Shawwala a ranar Asabar, hakan na nufin za a yi sallah ƙarama a ranar Lahadi, akasin haka kuma za a yi sallah a ranar Litinin.
Yanzu haka dai al’ummar Musulmi sun mayar da hankali wajen shirye-shiryen bikin sallah ƙarama na bana