Wata ɗaliba ta maka hukumomin makarantar Lead British a kotu bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda ake ‘cin zalin ta’ ya yaɗu a intanet.
Lauyoyin Namitra Bwala sun ce makarantar ta Lead British da ke Abuja, babban birnin ƙasar ta gaza samar da ingataccen yanayin karatu.
BBC ta ruwaito ta buƙaci makarantar da ta nemi afuwa a bayyane kuma ta biya ta diyyar naira miliyan 500, kwatankwacin dalar Amurka 350,000.
Bidiyon da ke nuna yadda wata ɗaliba ke zazzabga mata mari ya karaɗe shafukan sada zumunta a farkon wannan wata na Mayu.
Makarantar ta ce tana yin bincike kan lamarin kuma tana fatan ɗalibar za ta koma aji domin ci gaba da karatu